News
Wasu Yan bindiga sun yi garkuwa da mata takwas a Abuja
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rahotanni daga birnin Tarayya Abuja na cewa an yi garkuwa da wasu mata takwas a yankin Kuje.
Wannan labari na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 da sace mataimakin shugaban karamar hukumar Kwali da wasu mutane shida a kauyen Yewuti da ke Kwalin.
Matan da manoma ne an sace su ne a wata gona da ke kauyen Gwombe da ke masarautar Gwargwada a karamar hukumar Kuje.
Wani mazaunin Gwargwada, Usman Yakubu ya shidawa jaridar Daily Trust ta Najeriya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.
Ya kuma kara da cewa wasu ‘yan bindiga ɗauke da bindigogi kirar AK-47 ne suka yi awon gaba da matan, wadanda dukkaninsu matan aure ne da ke aikin girbi a gonakinsu.
Wani basaraken kauyen da ya zaɓi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace mutanen, sannan ya zargi cewa maharan ‘yan bindiga ne daga Kebbi da ‘yan banga Miyetti Allah suka tarwatsa a karshen mako.
Babu wani martani daga kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, kan lamarin kawo yanzu.
A wani labarin kuma Bayan Kwana 50 Masu garkuwa Sun sako dalibar jami’a
Wasu da ake zargin mayakan ‘yan aware ne daga yankin renon Ingilla na Kamaru sun kashe kimanin mutum tara a wani samame da suka kai a wani ƙauye da ke yankin yammacin kasar.
Harin ya afku ne a wata kasuwa da ke sashen gudanarwa na Galim, mai tazarar kilomita 15 daga yankin Arewa maso Yamma mai fama da rikici inda ‘yan awaren yankin renon Ingila ke fafatawa da sojojin jihar.
Moïse Mbazoa, wani ma’aikacin yankin, ya tabbatar da asarar rayuka da jikkata wasu, inda ya ce maharan sun yi garkuwa da mutane tare da sace babura.
Duk da rashin samar da hanyoyin dakile harin, an aike da dakarun soji daga garuruwan da ke makwabtaka da yankin.
Har yanzu dai ba a fayyace dalilin kai harin ba, amma hukumomi sun lura cewa wannan ba shi ne karon farko da ake zargin ‘yan aware ne suka kai hari Galim ba.
A cikin abubuwan da suka faru a baya, sun kai hari ga cibiyoyin gwamnati, suna yin garkuwa da mutane, da kuma neman kudin fansa.
Wannan lamari dai ya biyo baya makonni bayan da wasu da ake zargin ’yan aware ne suka kashe akalla mutum 20 a garin Mamfe da ke yankin Kudu maso Yammacin yankin renan Ingila.
Yankin yammacin Kamaru, wanda galibin masu amfani da harshen Faransanci ne, yana da iyaka da yankin Arewa maso Yamma mai fama da rikici.
Garuruwa da ƙauyuka daban-daban a yankin Yamma sun fuskanci hare-hare daga ‘yan tawaye da ake kyautata zaton mayakan ‘yan aware ne da suka samo asali daga yankin renon Ingila mai makwabtaka.
