Connect with us

News

Kotu ta ce lauyoyin  Jamiyyar NNPP da APC su mayar da kwafin hukuncin a gyara – Farfesa Chidi Odinkalu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Tsohon shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa Farfesa Chidi Odinkalu, ya ce, alkalan kotun daukaka kara sun bukaci lauyoyin jam’iyyar NNPP da APC, su mayar kwafin hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Kano wanda ke ci gaba da tada kura yanzu haka sakamakon yadda kwafin hukuncin ya yi hannun riga da matakin da alkalan su ka yi a ranar juma’a da ta gabata.

Hukuncin da alkalan su ka yi ya jaddada matakin da kotun sauraran kararrakin zaben gwamnan jihar Kano wanda ya bai wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna nasara.

Wasu Yan bindiga sun yi garkuwa da mata takwas a Abuja

Sai dai kwafin hukuncin kotun da kotun daukaka kara ta bai wa lauyoyin bangarorin biyu a jiya ya sha banbam da abin da alkalan su ka furta a ranar juma’a da ta wuce.

Kwafin hukuncin dai ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu nasara a daukaka kara da ya yi, har ma kotun ta bukaci jam’iyyar APC da ta biya shi diyyar Naira miliyan daya.

Advertisement

Wannan lamari dai yana ci gaba janyo cece-kuce, inda a nata bangaren jam’iyyar APC ta bayyana cewa, kuskure aka samu wajen rubuta takardar.

Sai dai da ya ke tsokaci kan lamarin da safiyar yau a shaginsa na X wato Twitter, Farfesa Chidi Odinkalu, wanda kwararren masanin shari’a ne, ya ce, ya samu labari daga majiya mai tushe cewa, kotun daukaka kara ta bukaci lauyoyin jam’iyyar APC da NNPP da su mayar da kwafin hukuncin domin a gyara kuskuren da aka yi.

Tsohon shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta Nigeria ya ce, wannan lamari ya nuna kara yadda cin hanci da rashawa suka samu gindin zama a bangaren shari’a.

“Idan mutum zai nazarci wannan tirka-tirka kan shari’ar zaben gwamnan jihar Kano, zai gane cewa, akwai lauje cikin nadi, alamu sun nuna wannan kwafi na hukuncin shine matsayin da alkalan suka dauka kan wannan batu, amma an canja musu raayi suka fadi wani hukuncin na daban a ranar juma’a da ta wuce” a cewar Farfesa Chidi Odinkalu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending