News
An kama wani mutum mai shekaru 53 bisa laifin yin lalata da kananan yara masu tabin hankali
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum mai shekaru 53 mai suna Usman Ahmadu bisa zarginsa da cin zarafin wata karamar yarinya mai tabin hankali.
Usman Ahmadu, wanda aka ce ya fito daga Maiduguri a jihar Borno, yana zaune ne a matsayin dan gudun hijira, IDP, a unguwar Saminaka da ke wajen Yola, a karamar hukumar Yola ta Arewa.
Najeriya Za Ta Fara Fitar Da Tataccen Mai Kasar Waje A 2024 —NNPCL
Yanzu haka rundunar ‘yan sandan jihar, Usman Ahmadu ya amsa laifin yin lalata da yarinyar mai tabin hankali har sau hudu, tun daga shekarar 2021.
Sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar wacce ta bayyana lamarin, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Sanarwar wacce jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya saki da safiyar Alhamis, ta ruwaito CP din yana bada tabbacin cewa babu wata maboya ga masu aikata laifuka kamar yanda Jaridar Daily Post ta ruwaito.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
