News
Sojojin Isra’ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar sojin Isra’ila ta tsare aƙalla Falasɗinawa 40 a wani samame da ta kai Yammacin Kogin Jordan da safiyar ranar Alhamis, a cewar Ƙungiyar Fursunoni ta Falasɗinawa.
Trt Afirka ta ruwaito cewa Kungiyar ta Falasɗinu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan Falasɗinawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.
Rashin yin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP
Tashin hankali na ƙaruwa a Yammacin Kogin Jordan a yayin da sojojin Isra’ila ke kai hare-hare Zirin Gaza tun bayan harin ba-zatan da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma Rashin yin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP
Hamas ta yi ikirarin cewa mayakanta ne suka kaddamar da harin Birnin Kudus da safiyar yau, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram.
Cikin sanarwar, Hamas ta ce ”ta kai hari ne saboda mayar da martani kan laifukan da ake aikata wa al’umominta ta hanyar mamaya,” tana mai kafa hujja da ayyukan sojin Isra’ila a Gaza da yadda ta ce ana muzgunawa Falasdinawa a gidajen yarin Isra’ila.
Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ambato sanarwar kungiyar na kira ga mambobinta da su ”ci gaba da fadada juriya”.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
