Connect with us

News

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Gabatar Da Biliyan 300 A Matsayin Kasafin Kudin 2024

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya mika wa majalisar dokokin jihar daftarin kasafin kudin shekarar badi da yawan su ya kai Naira biliyan N300,219,705,820.60.

Da yake jawabi a zauren majalisar, gwamnan ya ce, an yi hasashen Naira biliyan N178,878,512,477.49 kwatankwacin kaso 59.6 cikin dari zai tafi wajen gudanar da manyan ayyuka, yayin da kuma Naira biliyan N121,341,193,343.11 kwatankwacin kaso 40.4 na kasafin zai tafi wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.

Advertisement

 

Sojojin Isra’ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan

Ya ce, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samar da shugabanci na gari.

Advertisement

Ya gode wa majalisar dokokin jihar bisa hadin kai da suke bai wa gwamnatinsa tun a wa’adinsa na farko.

Ya nemi da su kara ba shi hadin kai a wannan lokacin domin dora ayyukan ci gaba a jihar.

Advertisement

A cewarsa, a zamaninsa na farko sun cimma muhimman nasarori, don haka suke fatan cewa a zangonsu na biyu za su kara himma domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Leadership ta ruwaito cewar gwamnan an tsara kasafin na 2024 domin bangarorin kiwon lafiya, ilimi, gona, tsaro na daga cikin muhimmanan bangarorin da suka samu kaso mafi tsoka a kasafin badin.

Advertisement

A nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar na Bauchi Hon. Babayo Muhammad Akuyam, ya bada tabbacin cewa majalisar za ta nazarci kasafin tare da yin abin da ya dace domin amincewa da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan da suka dace a Jihar Bauchi.

A wani labarin kuma Sojojin Isra’ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan

Advertisement

Ƙasar Afrika ta Kudu ta sami gudummawar Jenaretar samar da wutar lantarki guda 450 daga Ƙasar China domin magance matsalar ƙarancin wutar lantarki a ƙasar.

Wannan gudummawar wani bangare ne na shirin ba da taimako na fasaha da kasashen China da Afirka ta Kudu suka rattabawa hannu a yayin taron BRICS na watan Agusta a birnin Johannesburg.

Advertisement

A cikin yarjejeniyar, China ta yi alƙawarin ba da gudummawar kayan aikin gaggawa na rand miliyan 167 (dala miliyan 8.9) da tallafin raya kasa na rand miliyan 500.

Afirka ta Kudu dai na fama da matsalar katsewar wutar lantarki lamarin da ya haifar da takaici matuka.

Advertisement

Miliyoyin mutane suna kasancewa cikin duhu a kowace rana – wani lokaci har na tsawon sa’o’i 10 – a birane da garuruwa a fadin Afirka ta Kudu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending