Connect with us

News

Yan sanda  sun cafke wasu mutane takwas da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Jihar Kaduna 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wasu mutane takwas da ake zargi da yin garkuwa da mutane a kewayen Maigana Janar da ke karamar hukumar Soba a jihar Kaduna

Punch ta ruwaito cewa Hakan ya fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mansur Hassan, a Kaduna ranar Alhamis.

Advertisement

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Gabatar Da Biliyan 300 A Matsayin Kasafin Kudin 2024

A cewarsa, wadanda ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da mutane da sauran laifuka da suka shafi yankin a ‘yan kwanakin nan.

Ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Musa Garba, ya huri  jami’an hukumar da kuma jami’an rundunar da su kai farmaki kan masu aikata miyagun laifuka da ke addabar mutanen jihar a daidai lokacin da bukukuwan Kirsimeti ke karatowa.

Advertisement

A wani labarin kuma Gwamnan Jihar Bauchi Ya Gabatar Da Biliyan 300 A Matsayin Kasafin Kudin 2024

Shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi na COP28, kuma babban jami’in kamfanin man fetur na Hadaddiyar Daular Larabawa, (Adnoc) Sultan al-Jaber ya musanta zargin yin amfani da taron wajen kulla cinikin man fetur da iskar gas.

Advertisement

Ya musanta bayanan wasu takardu da aka fallasa.

Gidan rediyon BBC ya ruwaito a ranar Litinin cewa wasu takardu da aka fallasa, sun bayyana shirin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi, na tattaunawa da kasashen duniya 15 a kan batun man fetur.

Advertisement

Al-Jaber ya bayyanawa wani taron manema labarai cewa, irin wadannan zarge-zargen na da nufin zagon kasa ne ga shugabancinsa na COP28, yayin da BBC ta tsaya tsayin daka a kan rahoton da ta bayar na bincike.

A yau ne aka bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na Cop28, inda shugabannin ƙasashen duniya suka fara hallara a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending