Connect with us

News

Kotu ta yankewa sojan daya kashe gwani aisami hukuncin kisa ta hanyar RATAYA

Published

on

Mallam Goni Aisami Gashu'a,

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Babbar Kotun dake zamanta a Potiskum ta jihar Yobe, ta yankewa Sojan da ya kashe Mallam Goni Aisami Gashu’a, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Haka kuma abokin Sojan da aka yi kisan a gaban sa an yanke masa hukuncin zaman gidan Kaso na Shekaru Goma.

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Buƙaci A Gaggauta Ƙaddamar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Jihar Kaduna

A lokaci guda kuma Kotun ta bayar da Umarnin Mayar da Bindigar zuwa gidan Soji, bisa tsarin dokar Kasa, a lokaci guda kuma aka mayar da Motar Sheikh Goni Aisami, zuwa ga iyalan sa.

Idan baku manta ba a shekarun baya Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Sojoji suka tare Gwani Aisami a kan hanya suka yi masa kisan gilla da niyar sace Motar sa, wanda aka dauki lokaci ana gudanar da bincike.

Advertisement

A wani labarin kuma Sheikh Dahiru Bauchi Ya Buƙaci A Gaggauta Ƙaddamar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Jihar Kaduna

Qatar na ci gaba da aikin gyara yarjejeniyar tsagaita wuta da ta ruguje tsakanin Isra’ila da Hamas, da kuma matsa lamba kan kawo karshen yaƙin Gaza gaba daya, in ji shugabanta, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.

“Muna ci gaba da aiki don ganin an sabunta yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da kuma rage radadin mutanenmu a Zirin Gaza, amma tsagaita wuta ba shine hanyar magance matsalar ba, buƙatarmu a kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya.”

Qatar ce ke jagorantar shawarwarin da bangarorin biyu suka yi, wanda ya kai ga tsagaita buɗe wuta na tsawon mako guda har zuwa ranar Juma’a.

Tun bayan kawo karshen yarjejeniyar – inda bangarorin biyu ke zargin juna da rugujewarta – Isra’ila ta zafafa kai hare-hare a Zirin Gaza a wani ɓangare na burinta na kawar da kungiyar Hamas.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending