Connect with us

News

Kungiyar Kwadago Ta Yi Fatali Da Yunkurin Cefanar Da Kamfanin Samar Da Lantarki Na Kasa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Kungiyar Kwadago ta kalubalanci shirin da gwamnatin tarayya ke yi sake fasalin kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar kula da Kamfanonin Gwamnati ta bayyana shirin sayar da kashi 40 na hannun jarin gwamnati a kamfanonin rarraba wutar lantarki a kasuwar hada-hadar jari ta kasa a sabuwar shekara ta 2024.

Advertisement

Zamu Dage Takunkumin Da Muka Saka Wa Kasar Nijar Akan Sharadi Guda -ECOWAS

A cikin wata takardar bayan taro da shugaban kungiyar kwadago ta kasa kwamared Joe Ajaero ya fitar a ranar Talata, ya ce ‘yan Najeriya sun sha jin irin wannan labarin tsawon shekaru da suka gabata, ba tare da ganin wani kyakykywan sakamako ba, bayan an cefanar da kadarorin gwamnati saima karin wahalhalu da tsarin ke janyo wa al’ummar Najeriya da tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa dalilin da ya sa ake shirin sake fasalin kanfanin samar da hasken lantarkin na kasa TCN, nada alaka da ganin an baiwa wasu manyan masu rike da madafun iko,a kasar nan damar karbe ikon tafiyar da harkokin lantarkin a Najeriya domin suci karensu ba bu babbaka.

Advertisement

A wani labarin kuma Zamu Dage Takunkumin Da Muka Saka Wa Kasar Nijar Akan Sharadi Guda -ECOWAS

Yayin da rikicin siyasa ke daɗa ƙamari a Jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya, kwamishinan shar’a kuma babban atoni na jihar, Farfesa Zacchaeus Adangor ya ajiye aiki.

Advertisement

Sai dai a wasikarsa ta ajiye aiki, Adangor ya faɗa wa Gwamna Similanayi Fubara cewa ya ɗauki matakin saboda wasu dalilai na ƙashin kai.

Adangor wanda ya riƙe muƙami a gwamnatin baya ta Nyesom Wike, ya yaba wa gwamna Fubara saboda ba shi damar yin aiki a ƙarƙashinsa.

Advertisement

Ƙurar rikicin siyasa ta turnuƙe a jihar ta Rivers tun bayan da aka fara samun saɓani tsakanin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike da gwamnan jihar Similanyi Fubara.

Lamarin da ya kai ga wakilan majalisar dokokin jihar, waɗanda ke biyayya ga Wike sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Advertisement

Baya ga haka nan an rushe ginin zauren majalisar, inda gwamnatin jihar ta kafa hujja da cewa ta yi ne a ƙoƙarin yin gyara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending