Connect with us

News

Zamu Dage Takunkumin Da Muka Saka Wa Kasar Nijar Akan Sharadi Guda -ECOWAS

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Mista Sidie Tunis, Kakakin Majalisar ECOWAS, ya ce za a dakatar da hukuncin da aka yanke wa Jamhuriyar Nijar, idan har gwamnatin soja ta saki Shugaba Mohamed Bazoum.

Shugaban majalisar ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da tawagar mutane 19 daga kungiyar ‘yan Afrika suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja.

Babbar Magana: Ƙasar Jamus Ta Kirkiro Injin Kyankyasa Jarirai. 

Ziyarar dai ita ce ta sanya majalisar ta goyi bayan dage takunkumin da aka kakabawa Nijar domin rage radadin da talakawa ke fuskanta a kasar.

Shugaban majalisar ya bukaci tawagar da ta saki Bazoum da iyalansa ba tare da wani sharadi ba tare da sanya wani dan gajeren lokaci don mayar da kasar bisa tsarin mulkin kasar.

Advertisement

Daily Post ta ruwaito cewa cewar Tunis, ba tare da la’akari da yunƙurin da ƙungiyar ta yi ba, ba a sami wani sakamako mai kyau ba tun bayan da gwamnatin mulkin soja ta kawar da zaɓen dimokuradiyya a Nijar.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending