Connect with us

News

Hukumar INEC Ta Shirya Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihar Kano

Published

on

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa(INEC) reshen Jihar Kano ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi a kananan hukumomin Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garin Malam da Rimin Gado/Tofa na majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a cikin watan Fabrairu.

Advertisement

Kwamishinan zaben jihar, Abdu Zango ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a hedikwatar hukumar da ke Kano a ranar Talata.

Mutum 6 Sun Kone, 4 Sun Jikkata A Harin Boko Haram A Jihar Borno

“Mun shirya tsaf domin gudanar da zaben tare da kwararru wanda jami’an zabe a shirye suke su gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi shida na jihar.

Advertisement

“Za mu gudanar da zabe a rumfunan zabe 66 a fadin kananan hukumomin shida.

“Duk mutumin da ba shi da katin zabe ba zai yi zabe a kananan hukumomin ba,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce tuni hukumar ta tura wasu muhimman kayayyaki ga daukacin kananan hukumomin da abin ya shafa.

Leadership ta ruwaito cewa  za a yi amfani da na’urar BVAS a yayin sake gudanar da zaben da nufin tabbatar da sahihin zabe.

Advertisement

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar kan gudanar da zaben cike gurbin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel ya ce sun shirya samar da tsaro a dukkan harkokin zabe a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Advertisement

Gumel wanda ya samu wakilcin CSP Hamma Abdullahi, ya ce ‘yan sanda za su tura jami’an tsaro kowace rumfar zabe domin bai wa mazauna kananan hukumomin shida.

Ya gargadi shugabannin jam’iyyun siyasa da za su shiga zaben da su ja hankalin magoya bayansu da su guji tada tarzoma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending