Politics
Idan Kwankwaso Ya Ce Magoya Bayansa Su Faɗa Wuta, Fiye Da Rabin Al’ummar Kano Za Su Shiga –Buba Galadima
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jigo a jam’iyyar NNPP Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa idan Rabi’u Kwankwaso ya ce magoya bayansa su faɗa wuta, to rabin mutanen jihar Kano ne za su faɗa cikin wuta saboda yadda su ka baiwa Kwankwason yadda.
Injiniya Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV ya yi da shi.
Rufe iyakar Jamhuriyar Nijar yana cutar da tattalin arziƙin Najeriya — Sanata Aliero
“Idan yanzu Kwankwaso zai ce magoya bayansa su fada wuta su mutu, ina gaya maka rabin mutanen Kano za su faɗa saboda sun yarda da shi”
Haka kuma jigon jam’iyyar NNPP ɗin ya yi zargin cewa akwai wasu jagororin jam’iyyar APC da ke ƙoƙarin ɓata sunan tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso.
“Akwai wasu shugabannin jam’iyyar APC da ke biyan wasu ƙungiyoyi a NNPP suna ƙoƙarin ɓata sunan Kwankwaso, amma har yanzu sun kasa samun nasara.”
A ƙarshe Injiniya Buba Galadima ya bayyana Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin wani fitaccen ɗan siyasa da jama’a suka aminta da shi.