Connect with us

News

Za mu Dawo Kano idan yanayin kasuwanci ya daidaita —Shoprite

Published

on

DAGA  YASIR SANI ABDULLAHI

mamallakin katafaren shagon sayar da kayan masarurin nan mai suna ‘Shoprite Mall’ ya ce ficewar sa daga Kano na wucin gadi ne kawai saboda yana da shirin komawa jihar idan yanayin kasuwanci ya daidaita.

Advertisement

Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya sanar da rufe shagonsa na Ado Bayero da ke Kano a hukumance, wanda ya fara aiki a ranar 14 ga watan Janairun 2024.

Dalilin da ya sa na nemi afuwar ƴan Najeriya a karshen wa’adin mulkina – Buhari

Jaridar Prime time ta ruwaito cewa Katafaren shagon da ke harkokinsa a ‘Ado Bayero Mall’ ya ce, zai dakatar da harkokinsa ne saboda karayar tattalin arziki da shagon ke fuskanta da kuma yadda harkokin kasuwanci ke kara fuskantar tarnaki a sassan kasar nan.

Advertisement

Takardar sanarwa ta kuma ce, shawarar ficewa daga Nijeriya abin takaici ne kwararai da gaske amma kuma yana da matukar muhimmanci gare su, ‘Za mu dakatar da dukkan ma’aikatan da ke aiki a shagon da zaran mun daina aiki a jihar”.

Amma kuma bayan wadanna dalila da masu gudanar da shagon suka bayyana an kuma fahimci cewa, akwai wasu dalilai na karkashin kasa da suka sanya dole Shoprite ya dakatar tare da ficewa daga Nijeriya.

Advertisement

Bayanin ya nuna cewa, cikin manya-manyan dalilan sun hada da kudin haya na Naira miliyan 66 da suke biya a duk wata bayan kuma kudin wutar lantarki da na gudanar da shagon da na yau da kullum da kuma kudin albashin ma’aikata.

Kamfanin na biya naira miliyan 792 in aka hada da albashin ma’aikata da na wutar lantarki da sauransu.

Advertisement

Ya ce matakin ba ya nufin cewa Shoprite ba zai yi kasuwanci a Kano ba idan yanayin kasuwanci ya yi kyau, yana mai cewa “Kano babban birni ne da ke da damar yin kasuwanci.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending