News
Kungiyoyin kwadago na shirin fito-na-fito da gwamnatin tarraya kan albashi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyoyin kwadago Najeriya na shirin yin fito-na -fito da gwamnatin kasar da na jihohi bisa rashin samun wani ci gaba a game da mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati, kuma sun nuna cewa akwai yiwuwar yajin aiki.
Mataimakin magatakardan kungiyar kwadago ta NLC a kasar, Chris Onyeka, wanda ya bayyana haka, ya ce yanzu ma’aikata na cikin ukuba, inda ba sa iya biyan kudaden hayar gidajensu da ma kudaden makarantar ‘yayansu saboda matsanancin tsadar rayuwa.
Daga ‘yar buguwa kaɗan, sai likitocin Super Eagles suka ce wai guiwa ta ce ta gurɗe’
Ya kuma koka cewa duba da yadda kudin sufuri ya karu da kashi 300, akasarin ma’aikatan gwamnati na tattaki ne zuwa wajen aiki.
A watan Yunin shekarar 2023, kungiyar kwadago ta bukaci a daga mafi karancin albashin ma’aikata daga naira dubu 30 zuwa dubu 250, tana mai cewa halin da ake ciki ne y a tilasta wannan bukata.
A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur jim kadan bayan da ya sha rantsuwar kama aiki, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta iya ci gaba da biyan wadannan makudan kudade ba, duba da cewa wasu ‘yan kalilan ne ke cin moriyar tallafin a maimakon ilahirin talakawan Najeriya.
Wannan mataki na Tinubu ya janyo tashin farashin man fetur zuwa kusan naira dari 7 a kan kowace lita, lamarin da ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki, musamman ma na abinci, wanda hakan ya jefa talakan kasar cikin ukuba.
