News
An Samar Da Magunguna Kyauta A Asibitin Yara Na Hasiya Bayero —Dr Nagoda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da siyan magunguna kyauta da kayan aikin dakin gwaje-gwaje na asibitin yara na Hasiya Bayero a wani bangare na alkawarin kai wa marasa galihu dauke a harkar kiwon Lafiya a Jihar Kano
A ziyarar da tawagar masu sa ido a asibitin yara na Hasiya Bayero, tawagar ta bayyana cewa ginin yana da kyau sosai, masu gudanar da aikin sun fuskanci kalubale amma sun gamu da wurin da babu magani, babu magunguna da sauran kayayyakin aikin yau da kullum. Wannan ci gaban ya sa gwamnan ya amince da sayan kayayyakin da ake bukata na miliyoyin nairori cikin gaggawa.
Wani Jirgi ya zame daga titinsa a filin jirgin birnin Ibadan
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami ar yada labarai ta hukumar Samira Suleiman ta turawa da Jaridar Inda
Sanarwar ta kara da cewa Wani wurin da aka ziyarta da daddare wanda kuma ya ke a shiyyar da Hasiya Bayero shi ne asibitin Imam Wali. Ƙungiyar ta sami wuri mai tsabta sosai da kuma ma’aikata masu kyau, tare da gamsuwa da Kulawar su ga marasa lafiya.
Manyan batutuwan da aka ci karo da su inda rashin isasshen haske.
Dokta Nagoda ya ba da umarnin a gaggauta sakin igiyoyin hasken rana zuwa ginin kuma ya dauki ma’aikata 10 na yau da kullun don ci gaba da kokarin hukumar a cikin Asibitn.
Asibitin haihuwa na Marmara ya kuma karbi tawagar da daddare wanda kafin ziyarar an riga an shirya yin wani gagarumin gyare-gyare a wasu domin haduwa da zama a matsayin daidaitaccen asibitin haihuwa tare da aikin kula da lafiya na awa 24.
Hukumar kula da asibitocin jihar Kano tana da jimillar kayayyakin aiki guda 48 zuwa shiyyar 15 tare da manyan daraktoci shiyya a matsayin shugabannin wadannan cibiyoyin. Ya kara da cewa, “Za mu kawo rahoton shiyya-shiyya ga jama’a, hakan zai yi daidai da tsarin gwamnati na kawo sauyi a bangaren kiwon lafiya,” in ji shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
