Connect with us

Sports

AFCON : Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Ta Cire Masar Daga Gasar Cin Kofin Afirka

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD BASHIR 

Golan Masar Mohamed Abou Gabal ya barar da fenareti a bugun daga kia sai mai tsaron gida a wasan da Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo ta yi nasara da ci 8-7 bayan sun yi canjaras 1-1 a karawar matakin sili-daya-kwale na AFCON da suka yi ranar Lahadi a San Pedro .

Advertisement

Fenaretin da Abou Gabal ya buga ya daki ‘fol’ yayin da Lionel Mpasi ya zura fenareti a ragarsa lamarin da ya fitar da kasar da ta ci gasar AFCON sau bakwai daga gasar ta bana a filin wasan Laurent Pokou, inda ‘yan Kongo suka barke da murna.

Makomar Masarautun Kano Ta Fara Tayar Da Kura A Jihar

Ranar Juma’a ne dai Kongo za ta kara da Guinea a Abidjan.

Advertisement

Meschack Elia ya zura wa Kongo kwallo a ragar Masar a lokacin da ya ci kwallo da kai, sai dai kuma bai wuce minti tara ba Masar ta farke kwallon ta hannun Mostafa Mohamed wanda ya zura kwallo a ragar Kongo ta bugun fenareti .

An bai wa dan wasan tsakiyar Masar Mohamed Hamdy jan kati a karin lokaci inda ‘yan wasan Pharaohs, wandanda gwarzonsu Mohamed Salah yale jinya, suka daina kai samame, kuma suka tsare gida har wasan ya kai ga matakin bugun fenareti.

Advertisement

 

Rashin iya karkare wasa a lokaci

Advertisement

Shekara 50 da ya wuce ne dai Kongo ta doke Masar a gasar cin kofin Afirka a matakin dab da na karshe kuma Kongo ta samu ta lashe kofin na wancan shekarar.

Wasan ya kasance canjaras na hudu da kasashen suka yi a jere a Côte d’Ivoire a wannan shekarar, ko da yake wannan ne canjaras na shida a jere da Masar ta yi tun gasar cin Kofin Afirkan da aka yi a Kamaru, kuma lokaci na biyar a jere da Masar take kai wa matakin karin lokaci a zagayen sili-daya-kwale.

Advertisement

 

Rashin zura kwallon da za ta raba gardama ya sake damun Masar don ba su iya karkare wasan cikin minti 90 ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

TRT Afrika

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending