News
Sirikar Nasir El-Rufa’i ta yi barazanar hukunta matan Arewacin Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sirikar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i wato A’isha Habibu ta yi barazanar hukunta matan Arewacin Najeriya saboda yadda suke yada gulmace-gulmace a shafukan sada zumuta bayan wata ta tsokane ta a shafin Instagram
Rikicin na shoshiyal midiya ya samo asali ne bayan wata mai suna Zainab ta yi wa A’isha katsalanda a rayuwarta ta aure, tana tambayar ta kan dalilin rashin ganin hotunanta da mijinta, Bello El-Rufa’i a shafukan sada zumunta akai-akai.
Wannan tambayar ce ta harzuka A’isha wadda ta mayar da martanin cewa ” rayuwar aurenta ba ta fallasa ba ce kamar Yadda RFI Hausa ta rawaito
A cewar ta tace Ashe haka muka lalace a matsayinmu na al’umma? Kullum, ina yin addu’a ga ‘yan uwana ‘yan Arewa don ganin rayuwarsu ta inganta. Kar ku bari gulma da tsegumi da munafinci su mamaye rayuwarku. Inji A’isha.
Kazalika sirikar ta El-Rufa’i ta kalubalanci Zainab kan cewa, in ta isa, ta zo ta lakace mata hanci gaba da gaba kuma a bainal jama’a da irin wannan kalmar, inda ta ce, a nan za ta gane kurenta.
A cikin shekarar 2023 ne, A’isha ta auri dan tsohon gwamnan Kaduna, kuma ita ‘ya ce ga Kanar Habibu Shu’aibu, tsohon kantoman soja a jihohin Filato da Niger da ke Najeriya.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
