Connect with us

News

Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin halastaccen gwamnan jihar Adamawa.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin halastaccen gwamnan jihar Adamawa.

Mai shari’a John Okoro wanda ya shirya kuma ya karanta hukuncin a ranar Laraba ya yi watsi da ƙarar da ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aisha Dahiru wace aka fi sani da Binani ta shigar kan rashin cancanta

An kashe mata da mijin da suka halaka yaransu don su ji daɗin soyayya

A yayin da kotun ta yi watsi da ƙarar, kwamitin alƙalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro ta bayyana cewa, abin da Kwamishinan Zabe (REC), Hudu Ari ya aikata wani abu ne na rashin gaskiya da kuma aikata laifi.

Okoro ya ci gaba da cewa, babban jami’in zaɓe na jihar ne ya kamata ya bayyana sakamakon zabe, domin a kaucewa hargitsi da rudani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending