News
An kashe mata da mijin da suka halaka yaransu don su ji daɗin soyayya
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Ƙasar China ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da matarsa bisa laifin kashe ƙananan ‘ya’yansu biyu domin su ji daɗin soyayya da more rayuwarsu.
Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin kasar.
Wata gobara ta lalata shaguna da dama tare da kashe mutum daya a babbar kasuwar Zamfara
Mutumin dai ya jefar da diyarsa mai shekaru biyu da dansa mai shekara daya daga tagar wani gida, inda suka yi kokarin bayyana mutuwarsu a matsayin hadari.
Hukuncin kisan ma’auratan ya ɗauki hankalin jama’a sosai a shafukan sada zumunta na kasar, inda da yawa ke ganin hukuncin ya yi daidai da laifin da suka aikata.
Advertisements
