News
Wata gobara ta lalata shaguna da dama tare da kashe mutum daya a babbar kasuwar Zamfara
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Wata gobara ta lalata shaguna da dama tare da kashe mutum daya a babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar Talata a bangaren kayan daki na babbar kasuwar jihar.
An yanke wa Imran Khan da matarsa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14
A cewar kwamandan hukumar kashe gobara ta Najeriya, sabuwar ofishin kasuwa, Hamza Mohammed, wani mai shago wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya mutu a lokacin da yake kokarin shiga shagonsa domin kashe gobarar.
Jami’an kashe gobara na hukumar kashe gobara ta jihar sun yi ta fafatawa don hana gobarar yaduwa zuwa wasu shaguna.
Duk da haka, shaguna da yawa abin ya shafa.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
