Connect with us

News

Lagos ta shiga sahun biranen Afrika 10 mafiya aikata manyan laifuka

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wasu alkaluma da sashen tattara bayanan kasashe na Numbeo ya fitar game da faruwar manyan laifuka ya bankado wasu biranen nahiyar Afrika 10 da suka yi kaurin suna wajen aikata manyan laifukan.

A wani dogon sharhi da Numbeo ya yi game da karuwar aikata manyan laifuka, ya alakanta matsalar da matsanancin talaucin da ya addabi kasashe wanda a lokuta da dama kan kange yara daga damar iya samun ingantaccen ilimi baya ga rashin abinci.

Advertisement

A cewar Numbeo wadannan matsaloli sun yi tarayya wajen ta’azzara aikata manyan laifi ba kadai a nahiyar ta Afrika ba har ma da sauran sassan Duniya.

Kundin alkaluman na Numbeo ya ce biranen Afrika 10 su ke matsayin kan gaba a nahiyar wajen aikata manyan laifuka wadanda suka kunshi kisan kai ta’ammali da miyagun kwayoyi garkuwa da mutane baya ga fashi da makami.

Advertisement

Alkaluman dai sun sanya birnin Pretoria na Afrika ta kudu a matsayin mafi kololuwar aikata manyan laifukan da kimanin kashi 81.8 sannan birnin Durban duk dai a Afrika ta kudun da a matsayin na 2 da kashi 80.9.

Na 3 a cikin jerin biranen shi ne Johannesburg a Afrika ta kudun da kashi 80.7 sannan birnin Port Elizabeth a matsayin na 4 da jumullar aikata manyan laifuka kashi 77.0 kan Cape Town duk dai a Afrika ta kudun da kashi 73.5.

Advertisement

Sauran biranen da suka yi kaurin suna wajen aikata laifukan akwai jihar Lagos ta Najeriya a matsayin ta 5 da kashi 68.0 sannan Windhoek a Namibia da kashi 67.6 a matsayin ta 7.

Birni na 8 a cikin jeri shi ne Harare a Zimbabwe da kashi 61.0 sannan Nairobi a Kenya matsayin na 9 da kashi 59.1 sai birni na karshe kuma na 10 wato Casablanca a Morocco da kashi 54.4.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending