News
‘Yan Kasuwa A Kano Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Akan Yawan Hauhawar Farashin Kayayyaki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dangane da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, ‘yan kasuwa sun koma yin addu’o’i don neman taimakon Allah a jihar Kano.
Yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga yanzu zuwa Disamba 2023 ya tsaya da kashi 28.92 cikin dari kuma ya karuwa tsawon watanni 11 a jere.
Yan Najeriya na kara nuna damuwar su game da hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Muna So A Biya Mafi Karancin Albashi Naira Dubu 400 – Kungiyar NLC
A cikin wani faifan bidiyo, an ga wasu gungun ‘yan kasuwa suna gudanar da addu’o’i na musamman a kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano, babbar kasuwar tufafi a Najeriya
Rahotanni na nuni da cewa an nadi bidiyon ne a ranar Laraba yayin da ‘yan kasuwar da abin ya shafa ke gudanar da addu’o’i a titin Bayajidda da ke kasuwar Kantin Kwari a cikin birnin Kano.
A cikin dogon faifan mai minti 1:45, an ji muryar wani mutum, wanda ake kyautata zaton dan kasuwa ne, wanda gidan ke da shaguna sama da 30,000, yana mai cewa sun shiga taron addu’a na musamman ne domin neman taimakon Allah a cikin mawuyacin halin da ake ciki a kasuwar dama kasa baki daya.
Muryar ta ce sun gudanar da addu’o’in ne domin neman tuba daga Allah kan tabarbarewar tattalin arzikin da ke addabar Najeriya.
Muryar ta koka kan yadda farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabo a kasar, inda ta ce, “A yau mafi kankantar Shadda ita ce Naira 8,000, yayin da Atampa Rubber ta kai N3,000.”
Mutumin da ke cikin faifan bidiyon ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su yi koyi da ‘yan kasuwar ta hanyar komawa ga Allah.
“A yau, mun yanke shawarar gudanar da wannan taro na musamman na addu’a domin neman taimakon Allah a cikin wannan mawuyacin hali da muka tsinci kanmu a ciki.
“A yau, farashin mafi kankantar Shadda ya kai Naira 8,000. Rubber Atampa N3,000. Buhun sukari da shinkafa 50kg naira 70,000 kowanne.
“Shugabannin mu ba su yi mana adalci ba, kuma Allah zai hukunta ku. Kun nemi kuri’un mu. Mun shafe lokacinmu a cikin rana mai zafi don zabe ku kuma mun tabbatar da kuri’unmu a gare ku, amma wannan shine ladan da muke samu na zaben ku.
“Shugabannin mu kullum suna yin alkawuran karya ba komai a kasa. Kuna fakewa da sunan dalar Amurka don yaudarar ’yan Najeriya.
“Ba shugabanni kadai ba, ’yan kasuwa ma ke da laifi. Sun ba da gudummawa ga matsalolinmu. Mun bar su wurin Allah,” in ji mutumin.
