Connect with us

News

Ƴan sanda sun damƙe ƴan damfarar da suka damfari ɗaliban jami’ar Kaduna kuɗaɗen makarantansu har naira miliyan 60

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Ƴan sanda sun damƙe ƴan damfarar da suka damfari ɗaliban jami’ar Kaduna KASU kuɗaɗen makarantansu har naira miliyan 60

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wasu ‘yan damfara ta yanar gizo su uku da suka damfari daliban jami’ar jihar Kaduna, KASU kudaden makarantar su har naira miliyan 60.

Advertisement

Zanga-zanga Ta Barke A Kasar Senegal Bayan Sanar Da Dage Zabe

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Mansir Hassan wanda ya sanar da haka a wata sanarwa a garin Kaduna ya ce ‘yan damfarar da suka hada da wani mai suna Muhammad Uthman Busari ɗan asalin kauyen Nariya dake, ɗan asalin jihar Kogi, da wani AbdulAzeez Hamza mazaunin Hayin Dan-Mani a jihar Kaduna da Noel Nims Audiya.

Premium Times ta ruwaito cewa Hassan ya ce wadannan mutane su rika damfarar daliban ne a lokacin da suka buɗe musu manhajar biyan kuɗaɗen makaranta da ake biya ta yanar gizo.

Advertisement

“Su kan karɓi kuɗaɗen ne daga hannun ɗaliban daga nan sai su ki biya cikin ainihin asusun jami’ar, amma kuma sai su basu shaidar biyan kuɗin makarantar cikakke.

Su kuma ɗaliban sai su kama gaban su. Haka suka rika yi duna ta tara kudade masu yawan gaske da sunan suna yi wa ɗalibai rajista ashe na boge ne.

Advertisement

“Sakamakon binciken da jami’an tsaron suka gudanar ya nuna cewa Shugaban ‘yan damfarar Muhammad Uthman Busari ya gina guda, ya siya mota, filaye a jihohin Kaduna da Kogi.

Gumel ya ce idan aka kammala bincike za a kai mutanen kotu domin a yanke musu hukunci.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending