Connect with us

News

Abin Da Yasa Kano, Jigawa Ba Su Fama Da Matsalar ‘Yan Bindiga -Shehu Sani

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

 

Advertisement

Shehu Sani, tsohon sanata, ya yi bayanin cewa za a iya magance matsalar tsaron Najeriya akalla cikin hanyoyi hudu

Tsohon dan majalisar ya yi bayanin cewa daya cikin hanyoyin da suka fi dacewa a yi yaki da rashin tsaro shine gwamnoni su kashe kudaden da ake turawa jihohinsu ta hanyoyin da suka dace

Advertisement

Ƴan sanda sun damƙe ƴan damfarar da suka damfari ɗaliban jami’ar Kaduna kuɗaɗen makarantansu har naira miliyan 60

Sani ya yi mamakin abin da yasa ba a samu ta’addanci ko ‘yan fashin daji ba a jihohi kamar Kano da Jigawa

Shehu Sani, tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisa ta takwas, ya bada shawarwari hudu ta yadda za a yi yaki da ta’addanci, ‘yan bindiga da masu garkuwa a arewacin kasar.

Advertisement

Da ya ke magana a zauren ‘space’ da Legit.ng ta yi a manhajar x a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairu, mai rajjin kare hakkin bil adaman ya yi tambayar mai yasa ba a samun ta’addanci a wasu jihohin arewa, musamman Kano da Jigawa.

 

Advertisement

SHEHU SANI YA BAYYANA HANYOYI HUDU DA ZA A MAGANCE TSARO A AREWA. 

 

Advertisement

Tsohon sanatan ya ce saboda gwamonin jihohin, tsawon lokaci, suna daukan batun tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba da muhimmanci, kuma suna kashe kudin tsaro

(Security Vote) da ake tura musu ba yadda ya dace.

Advertisement

 

A cewar tsohon sanatan, ‘Yan Najeriya ba za su jinjinawa Shugaba Bola Tinubu ba saboda kokari; mutane na son a kawar da ta’addanci, ‘yan bindiga da garkuwa da mutane baki daya ne, ya kara da cewa abin na bazuwa daga arewa zuwa kudu.

Advertisement

 

HANYOYI HUDU DA ZA A MAGANCE RASHIN TSARO A NAJERIYA, SHEHU SANI 

Advertisement

 

Ya kara da cewa hanya mafi dacewa don magance matsalar shine a dena tura kudi kawai. Maimakon hakan, a saka ido kan yadda ake kashe kudin da aka ware don tsaro.

Advertisement

 

Kuma, Sani ya ce a yi amfani da na’ura da mutane wurin tattara bayanan sirri don yaki da rashin tsaro, ya kara da cewa a duba me yasa kasashe kamar Benin da Jamhuriyar Nijar ba su fama da irin matsalar da Najeriya ke fama da shi.

Advertisement

 

Dan siyasan haifafan jihar Kaduna ya kuma bada shawarar cewa idan ba a kirkiri ‘yan sandan jihohi ba, toh, a rika tura ‘yan sandan tarayya zuwa jihohinsu na anihi saboda za su fi sanin lungu da sakuna kuma mutanensu za su yarda da su. Sani ya ce:

Advertisement

Akwai labarin nasarori a Najeriya; me yasa babu ‘yan bindiga a Kano? Me yasa babu ‘yan ta’adda a jihar Kano? Kuma wadannan jihohin arewa maso yamma ne. Saboda gwamnonin ba su wasa da batun tsaro.

An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye “Tun daga Kwankwaso zuwa Ganduje da yanzu Abba, ba su wasa da tsaro.

Advertisement

Kamata ya yi a kashe kudin tsaro (Security Vote) kan tsaro, ba rabawa magoya baya ba, ‘yan daban siyasa da harkokin siyasa. Idan munyi hakan, za mu dace.” Asali:

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending