Connect with us

News

Lokaci Yayi Da Za’a Kawo Karshen Musgunawa Fulani – Dakta Awwal 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gamayyar Kungiyoyin Arewa 593 daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya ( AREWA CONSENSUS MOVEMENT) sun bayyana cewa lokaci yayi da za’a kawo karshen matsalar musgunawa Fulani Makiyaya a fadin kasar nan.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin na Kasa Dakta Awwal Abdullahi Aliyu, shine ya bayyana haka Jim kadan bayan kammala wani taron kungiyar tayi da kungiyoyin Fulani da wasu kungiyoyi daga fadin Nijeriya wanda ya gudana a jihar Kaduna.

Kotu ta Sanya Rana domin sauraron daukaka karar Abduljabbar Nasir Kabara

Kungiyarsu ta himmatu wajen tabbatar da cewa an daina musgunawa Fulani da inda yace suma mutane ‘Yan kasa kamar kowa da kuma sauran ‘Yan Arewa da suke rayuwa a Arewacin Nijeriya dama kudan kasar .

” Mun gudanar da wannan taro ne domin tattauna matsalolin mutananmu daga Arewa da kuma ‘Yan Arewa da ke zama a kudancin kasar nan muga ya za’a yi a zauna lafiya wadanda aka zalunta muga ta Yaya za’a kwato musu hakkinsu su kuma wadanda sukayi zuluncin muga ya za’ayi a hukunta su domin bawa kowa Hakkinsu”

” Mun shiga gaba wajen ganin ya za’a warware bakin fentin da ake shafawa fulani wanda ake ganin kowanne Bafulatani dan ta’adda ne ko dan garkuwa da mutane ne saboda rashin adalci ne ayiwa al’umma guda daya jam’u wanda Bai kamata ba”

Advertisement

Kungiyar mu ta himmatu wajen tattaunawa da gwamnati muga yadda za’a warware matsalar dake tsakanin fulani da kuma Gano shin ta Ina ne matsalar take da kuma sanin su wanene ke da alhakin matsalar da kuma sanin yadda za’a magance matsalolin kuma insha Allah tattaunawar mu tayi Nisa akan hakan” inji shi.

Da yake bayani akan samar da jami’an tsaro na ‘Yan Sa kai, shugaban yace akwai alfanu a cikin tsarin muddin zasu bi dokokin da suka kamata wajen tallafawa harkar tsaron.

Ya kara da cewa idan har Askawaran tsaron irin na jihar Zamfara da Jihar Katsina zasu bi hanyar da suka kamata, babu shakka za’a samu saukin matsalar rashin Arewacin Nijeriya Yana Mai cewa wuce gona da irin daga wurin jami’an tsaron sa kai shime Yana taimawa wajen Lalata lamuran tsaro.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending