Connect with us

News

Dantata Ya Ce Tsarin Shugabancin Firaminista Da Wasu ’Yan Majalisa Suke Nema Shi Ne Mafi Alheri Ga Najeriya 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN  TUKUNTAWA 

Shahararren dan kasuwan nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce tsarin shugabancin firaminista da wasu ’yan majalisa suke nema shi ne mafi alheri ga kasar nan.

Dantata, ya bayyana haka ne a lokacin da wasu ’yan majalisar wakilai karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni Kan Ƙalubalen Da Nijeriya Ke Fuskanta

Aminu Dantata ya ce, “Na gode da wannan ziyara, kuma ina yi wa wannan gagarumin gangami addu’ar samun nasara.

“Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da kasar nan saboda babu kashe kudin gudanarwa kaman tsarin shugaban kasa da muke bi.

“Ina fata za ku samu goyon bayan abokan aikinku, kuma ina rokon Allah Ya ba ku basira, Ya kuma yi muku jagora wajen cimma wannan kyakkyawan manufa ta taimakon kasar nan.

Advertisement

 

Karin bayani na tafe……

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending