Connect with us

News

Tsadar Rayuwa: Akwai karancin fitowar jama’a a jihar Kano yayin da kungiyar kwadago ta NLC ke shirin gudanar da zanga-zanga

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Akwai karancin fitowar jama’a a jihar Kano yayin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ke shirin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matsalar tattalin arziki da manufofin gwamnati ke jawowa.

Daily Trust ta ruwaito cewa zanga-zangar wadda aka shirya za ta fara da karfe 8 na safe har yanzu ba ta fara aiki da karfe 9:30 na safe a Kano ba, duk da cewa an fara gudanar da zanga-zangar a wasu jihohin.

Gwara na mutu da wannan rayuwar matsi da muke ciki”

Rahotanni na nuni da cewa shugaban kungiyar NLC na jihar, Kwamared Kabiru Inuwa ba ya nan a wurin taron na Race Course, har zuwa lokacin.

Daily Trust ta ruwaito cewa zanga-zangar NLC a baya a jihar ta kan samu cikakkar halartar kungiyoyin kwadago  kungiyoyi daban-daban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending