Connect with us

News

Kiran Ruwa: Ƙabilu Da Ba Su Ga Maciji Da Juna Sun Kashe Sojoji 16 A Harin Kwanton Ɓauna, Ciki Da Janar, Manjo Da Kaftin

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Wasu mazauna kauyukan da basu jituwa da juna sun kashe jami’ai 16 na runduna ta 181 ta Amphibious Battalion ta sojojin Najeriya da ke aikin samar da zaman lafiya a yankin Okuoma da ke karamar hukumar Bomadi a jihar Delta ranar Alhamis.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa wadanda aka kashe dai sun hada da kwamandan rundunar, Manjo biyu, kyaftin daya da sojoji 12.

Tsadar Rayuwa:  Gwamnatin Legas Ta Bayyana Rangwamen Kashi 25 Cikin 100 Na Kayan Abincin 

Mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro Tukur Gusau ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja.

Advertisement

Ya bayyana cewa an yi wa sojojin kwanton bauna ne tare da kashe su a lokacin da sukw kokarin kai ɗauki yayin ɓarkewar rikici tsakanin Okuama da Okoloba a Delta.

Birgediya Janar Gusau ya bayyana cewa, babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke wadanda ke da hannu a aikata wannan danyen aikin.

Advertisement

Ya kara da cewa an kai rahoton lamarin ga gwamnatin jihar Delta. “Sojoji, duk da haka, sun ci gaba da mai da hankali da kuma jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan. “Ya zuwa yanzu, an kama wasu yayin da ake cigaba da gudanar da bincike

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending