News
Abdul Ningi na da gaskiya, ƙadan ma ya bankaɗo, akwai da yawa binne a Kasafin

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Bayan fallasa wasu cushe da majalisar Dattawa ta yi wanda sanata Abdul Ningi ya ya yi da kuma hakan ya yi sanadiyyar dakatar da shi, Jaridar PREMIUM TIMES ta bi diddigin wannan zargi domin tabbatar da gaskiyar maganar.
Sanata Ningi ya ce akwai wasu ayyuka na akalla naira biliya 54 da aka cisa su cikin kasafin kuɗin 2024 wanda kuma wannan ayyuka ba su cikin kasafin farko da shugaban Tinubu ya mika wa majalisa.
Sanata Ningi da ke wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a kwanakin baya ya zargi shugabannin majalisar da yin cushen wasu ayyukan boge a cikin kasafin kudin 2024.
Bitar wasu takardu da ke kunshe da bayanai kan kasafin kuɗin da jaridar Premium Times ta samu da kuma nazarin kasafin kudin shekarar 2024 da aka yi sannan kuma da yi wa kasafin da a karshe majalisar ta amince da shi ya nuna cewa korafin sanata Ningi na bisa turbar gaskiya.
Idan ba a manta ba, Ningi ya yi zargin an yi cushen wasu ayyuka har 36 da kuɗin su ya kai naira biliyan 53, da ba a san a ina za a yi su ba kawai an lafta su ne a cikin kasafin kuɗin don a waske da ƙudin.
Misali Ningi ya yi korafin za ayi wasu ayyuka a karkashin Kwalejin Albarkatun Kasa ta Tarayya, Owerri, Jihar Imo, kuma za a kashe naira miliyan 500.
Ba a ce ga inda za a saka wannan aiki ba sai dai kawai wai wasu zaɓaɓun ayyukan cigaban ne za a yi da su karkashin ayyukan a wannan jami’a.
Da PREMIUM TIMES ta bincika ta gano babu wannan kasafi a cikin wanda shugaban Tinubu ya mika wa majalisa
Bayan haka wannan jarida ta bankado wasu ayyukan biliyoyin kuɗi da aka cusa cikin kasafin kuɗin 2024 karkashin ayyukan da za a yi a wannan jami’a da basu cikin kasafin da Tinubu ya mika a majalisa.
An cusa akalla ayyuka 14 da kuɗinsu ya kai naira biliyan 2.4 karkashin ayyukan da za a yi jami’ar.
Sai dai kuma ma, Ningi bai fallasa duka ba, binciken PREMIUM TIMES kan badakalar cushen a kasafin kuɗin 2024, ya banƙado wasu wurare da dama da aka lafta wa kuɗaɗe don yin cushe a kasafin kuɗin.
Sai kuma ganin cewa tun daga shugaban kasa zuwa mataimakin sa, Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da ministan kasafin kuɗi duk tsoffin ƴan majalisa ne, ba su ga laifin komai akan wannan cushe da ke zargin majalisar ta yi ba.
Ministan Kasafin kudi, Abubakar Bagudu ya bayyana cewa majalisun dokokin kasa na da damar yin kari a kasafin kuɗi doka ta basu wannan dama.
