News
Karyewar babbar gadar Baltimore ta gigita Amurka
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Masu aikin ceto na ci gaba da laluben mutanen da suka fada ruwa sakamakon karyewar gadar Baltimore mai nisan kilomita 2.57 da ke yankin gabar ruwan Patapsco na gabashin Amurka.
Jirgin ruwa mallakar wani kamfanin Singapore mai suna Dali ya rusa babbar gadar da ta ratsa gabar ruwan Patapsco da ke yankin gabashin Amurka. Gadar Francis Scott Key ta karye sakamakon jirgin ruwan ya daki guda daga cikin turakun gadar, wanda hakan ya haifar da mummunar hadari, kuma a halin yanzu ake ci gaba da neman mutanen da ake hasashen sun nutse cikin ruwa.
Ƙaruwar Hare-haren ‘Yan Bindiga:Na gaya wa Shugaban Ƙasa matsalolin Zamfara – Dauda Lawal
Yadda jirgin ruwa ya ruguza gadar Baltimore a AmurkaYadda jirgin ruwa ya ruguza gadar Baltimore a Amurka
Gwamnan jihar Maryland Wes Moore, ya ayyana dokar ta baci a yankin, a daidai lokacin da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin ceton ragowar mutanen da ake hasashen sun fada a cikin ruwa sakamakon karewar gadar.
Kwamishinan ‘yan sandan Baltimore Richard Worley da magajin garin birnin Brandon Scott da kuma shugaban hukumar kashe gobara James Wallace.Kwamishinan ‘yan sandan Baltimore Richard Worley da magajin garin birnin Brandon Scott da kuma shugaban hukumar kashe gobara James Wallace.
Rahotanni na cewa babu wanda ya samu rauni a ma’aikatan jirgin, sai dai hadarin ya tayar da hankulan al’ummar yankin na Patapsco da ke a gabashin Amurka da ma na sauran kasashen duniya.