News
Dalilin Da Ya Sa Ban Yi Musabaha Da Gwamna Abba Yusuf Ba – Ahmed Musa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles), Ahmed Musa, ya magantu kan cece-kucen da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta dangane da yadda ya yi mu’amala da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a ziyarar da ya kai gidan gwamnati a watan da ya gabata.
Leadership ta ruwaito cewa a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Musa ya durkusa wa gwamnan ba tare da yin musabaha ba, lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Gamboro Da Ke Maiduguri A Jihar Barno
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a shafinsa na X (Twitter), Musa ya fayyace cewa, matakin nasa ya samo asali ne daga al’adun mutuntawa na gari, maimakon yadda wasu ke ganin cewa, rashin mutuntawa ga Gwamna Yusuf.
Ya jaddada cewa, a al’adun Arewacin Nijeriya, ayyuka irin su durkusawa suna nuna girmamawa ga masu daraja.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
