News
Kotun Da’ar ma’aikata ta dakatar da Muhyi Magaji daga shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wani mataki da ka iya girgiza yunkurin jihar Kano na yaki da cin hanci da rashawa, Kotun da’ar ma’aikata ta dakatar Muhuyi Magaji daga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka gurfanar da Magaji a gaban kuliya bisa manyan zarge-zarge, da suka hada da saba ka’idojin da’a ga jami’an gwamnati, da yin rikici da juna, cin zarafin ofishinsa, da bayar da bayanan karya kan bayyana kadarorinsa.
Dalilin Da Ya Sa Ban Yi Musabaha Da Gwamna Abba Yusuf Ba – Ahmed Musa
Ana kuma zarginsa da cin hanci da karbar kyaututtuka.
Kotun ta goyi bayan wanda ya shigar da karar, inda ta umurci Magaji da ya ajiye mukaminsa na Shugaban Hukumar.
Ba zai iya cika aikinsa a Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ba har sai an saurari tuhume-tuhumen da ake yi masa, sannan a yanke hukunci.
Bugu da kari, kotun ta umurci gwamnan jihar Kano da sakataren gwamnatin jihar da su nada shugaban riko na hukumar domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar a wannan lokaci.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
