News
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kano Ta Maka Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, Matarsa, Hafsat Da Wasu Mutane 6 A Kotu Akan Zargin Cin Hanci Da Rashawa.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta maka tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, Hafsat Umar, Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a gaban kotu, bisa zarge-zarge 8 da suka hada da cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kudade da suka shafi biliyoyin naira.
Wannan yana kunshe ne a cikin takardar tuhuma mai kwanan wata 3 ga Afrilu, 2024 tare da lissafta jerin shaidu 15 masu gabatar da kara.
SOLACEBASE ta ruwaito cewa sauran wadanda ake kara a karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.
Details soon
Advertisements
