Connect with us

News

Wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta za su kara munana ta dalilin karin kudin lantarki —Atiku Abubakar

Published

on

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce karin kudin wutar lantarki zai kara haifar da matsaloli ga ‘yan Najeriya.

Hakan na kunshe ne ta cikin Sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce Gwamnatin Tarayya na sake fasalin ba tare  da wani isasshiyar shirin bayan gyara don rage radadin ba.

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi ya dakatar da kwamishinan ma’aikatar kasuwanci

Ya rubuta cewa: “Ƙarin kudin wutar lantarki ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cikin mawuyacin hali sakamakon janye tallafin da ake yi wa PMS .

“Gwamnati ba ta samu nasarar magance radadin da ke tattare da aiwatar da wadannan matakan ba, kuma a yanzu haka. Karin farashin wutar lantarki zai kara haifar da wahalhalu ga ‘yan kasar yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke karuwa.

 

Advertisement

 

Daily post

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending