Connect with us

News

Yadda wasu yara biyar suka mutu lokaci guda a Neja

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wasu yara biyar sun mutu a cikin wata mota da suka shiga suna wasa, inda motar ta kulle kanta suka kasa fita.

Solacebase ta ruwaito cewa lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi, an ce an sha famar neman yaran a unguwa alhali ba a san cewa suna kulle cikin motar ba, daga bisani aka gano su baki ɗayansu a mace.

Hukumar da ke kula da gidan gyaran hali a Kano ta ce kashi 70 cikin 100 na fursunoni a jihar ke jiran shari’a.

Shafin Tsalle Ɗaya ya ce iftila’in ya faru ne a Unguwar Albishiri da ke daura da yankin Gurara a hanyar Bida, Minna, Jihar Neja.

Majiyarmu ta ce huɗu daga cikin yaran mata ne, sannan ɗaya namiji.

An ce uku daga cikin yaran, yaran mutum guda ne wanda kuma su ke nan da Allah ya azurta iyayen da su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending