Connect with us

News

Karancin Man fetur: Ana Fuskantar Dogayen Layi A Gidajen Mai Jihar Kano 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

A baya-bayan nan ana wayar gari da ganin motoci sun kafa layi a gidajen mai yayin da wasu direbobi ke kokawa kan yadda farashin man ya tashi.

Advertisement

Binciken da jaridar Daily Trust ta yi a Abuja da Kano da Kaduna da Legas ya nuna cewa ana samun dogayen layukan mai a gidajen mai da dama.

Kimanin Fursunoni 118 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Suleja

A Abuja, babban birnin Najeriya, galibin gidajen man da ke ƙwaryar birnin ba su da man.

Advertisement

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu manyan gidajen mai sun rufe ƙofa inda suka ce ba su da mai.

Sai dai a gidajen man NNPCL cikin ƙwaryar birnin, ana samun mai sai dai akwai dogayen layukan motoci.

Advertisement

Tsirarun gidajen mai da ke da man kuma sun ƙara kuɗi da ya kai N750 kowace lita daya.

A Kano ma direbobi na shafe tsawon sa’oi a gidajen mai kafin su samu man.

Advertisement

An fi ganin layukan man a gidajen mai na NNPC a da ke Kofar Nasarawa da ke kan titin Ibrahim Taiwo.

A jihar Kaduna ma, an ga layukan mai a gidajen da ke sayar da shi.

Advertisement

Bbc Hausa ta ruwaito cewa haka  batun yake a Legas inda NNPC ke sayar da N560 duk lita ɗaya yayin da manyan dillalan mai ke sayar wa a kan N590 da N610.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending