Connect with us

News

Wata Gobara ta tashi a filin jirgin saman Legas

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta sauya wa jirage da tashin su waje cikin gaggawa daga sashin E na filin jirgin saman Murtala Muhammad (MMIA) sakamakon gobara da ta tashi.

Advertisement

Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar yau Alhamis bayan da aka samu hayaki a gadar E54.

Karancin Man fetur: Ana Fuskantar Dogayen Layi A Gidajen Mai Jihar Kano 

Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an hukumar ceto da kashe gobara a filin tashi da saukar jiragen sama sun yi gaggawar daukar matakan shawo kan gobarar da ta katse wutar lantarki a tsohon bangaren tashi da saukar jiragen na kasa da kasa.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa tsohuwar tashar ta fuskanci matsalolin gobara, wanda hakan ya sa ake rufe ta lokaci zuwa lokaci.

 

Advertisement

Hukumar ta FAAN a cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun daraktan hulda da jama’a da kare abokan mu’amala, Mrs Obiageli Orah, ta tabbatar da faruwar gobarar, inda ta ce cikin gaggawar jami’an kashe gobara na filin jirgin sun samu nasarar shawo kan lamarin.

 

Advertisement

Ta ce, “Da karfe 05:29 na safe, an gano hayaki yana ta turnukewa daga gadar E54, wanda hakan ya sa injiniyoyin lantarki suka katse wutar lantarki ga daukacin ɓangaren E.

 

Advertisement

“Rundunar ceto ta filin jirgin sama da masu kashe gobara (ARFFS) sun yi gaggawar zuwa wqjen, inda suka isa wurin da karfe 05:30 na safe.

 

Advertisement

“Abinda aka fara zargi shine tartsatsin wuta daga na’urar lantarki a matsayin musabbabin, amma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin tashin gobarar. Lamarin wanda ya rikide zuwa gobara, an shawo kan sa da karfe 06:41 na safe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending