News
Hukumar Hisbah ta fitar da Sabon Tsari Akan DJ A Wajen Bukukuwa A Jihar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramtawa maza DJ yin wasa a bukukuwan mata a fadin jihar.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan a wani taro da wakilan DJ na jihar.
Al’ummar Mazabar Gobirawa Na Cikin Matsanantiyar Damuwa Akan Tsayawar Aikin Fadada Asibitocin 3
Ya ce matakin ya zama dole domin a hana cakuɗu wa tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwa.
Sheikh Daurawa ya bayyana cewa daga yanzu mata ne kawai za a bari su gudanar da taron su na mata.
Ya ce, “A matsayinmu na jihar shari’ar Musulunci, ba abin yarda ba ne a ce mu bari a rika cakuduwar maza da mata a wuri guda. Irin wannan na karfafa yada lalata.”
A nasa jawabin, wakilin DJs din, Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da DJ Farawa ya yabawa hukumar bisa gayyatarsu da kuma ba su shawarwari kan sabbin tsare-tsare da hukumar ta bullo da su domin gudanar da harkokinsu.
Ya ce, “Mun yi farin ciki da gayyatar hukumar Hisbah zuwa ga kungiyar mu ta DJ. Sun ba mu ƙa’idoji a rubuce na yadda za mu kiyaye lokutan sallah da kuma wajibcin hana cakuduwar maza da mata a wajen taro.”
Ibrahim ya lura cewa duk DJs da ke gudanar da ayyukansu a jihar dole ne su bi sabbin ka’idojin da hukumar ta fitar don gujewa hukunci.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
