News
Mai martaba sarkin kano ya bukaci kungiyar matan yan sandan dasu kara himma wajen koyawa marayu da masu bukata ta musamman sana’oin dogaro da kansu.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR.JP ya bukaci kungiyoyin matan yan sandan kasar nan dasu kara himma wajen hada kan kungiyar matan yan sandan domin koyawa marayu da masu bukata ta musamman sana’oin dogaro da kansu.
Mai Martaba Sarkin ya bulaci hakan ne lokacin da kungiyar Matan yan sandan jihar kano Police Officers Wives Association suka kawo masa ziyara a fadar sa.
Mutane 15 Ne Suka Rasu Cikin Wanda Ake Zargin Wani Matashi Da Cinnawa Wuta Cikin Masallaci A Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero yace yaji dadin wannan ziyara da kungiya Matan yan sanda suka kawo masa tareda kudiurin da suke dashi na taimakawa marayu don su dogara da Kansu ba sai gwamnati ta basu aikin yi ba.
A nata jawabin Shugabar Kungiyar kuma Matar Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Hajiya Aisha Muhd Hussain Gumel tace tazo fadar Sarkin ne domin nuna goyon bayanta ga masarauta da kuma basu shawarwari domin cigaba kungiyarsu.
A wani cigaban kuma Mai Martaba sarkin na Kano ya kai ziyara asibitin Murtala fake cikin birnin Kano domin duba marasa lafiya wadanda wani matasa ya bankawa wuta a massalaci a dai dai lokacin da suke gabatar da sallar asuba garin gadam dake Larabar Abasawa a karamar hukumar gezawa.
Alhaji Aminu Ado Bayero Bayan nuna jimami da alhinin abunda ya faru yayi addu’ar fatan samun lafiya a garesu da kiyayewar afkuwar hakan.
Sarkin yayi addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasu yasa aljanna madaukakiya itace makoma a garesu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
