News
Kasuwancin Crypto: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kano Ta Kama Wasu Jami’an Ma’aikatar Lafiya Da Suka Kwashe Kudin Rajistar Dalibai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama tare da tsare wasu ma’aikatan ma’aikatar lafiya ta jihar Kano 3 bisa zargin karkatar da kudaden rajista na daliban makarantar jinya 186 da ya haura N5m
Rahotanni na nuni da cewa wadanda aka kama sune Tsohuwar Darakta, Kwalejin Kimiyyar Ma’aikatan Jinya, Danbatta, Hajiya Hasiya Sani, Akawun Makarantar Madobi ta Nursing, Ahmed Zubairu da Focal Person a Madobi, Fadilu Aliyu.
Da Dumi Dumi : Shugaba Tinubu ya nada Dakta Nasiru Yusuf Gawuna A Mukami
Da yake tabbatar da kama mutanen uku ga jaridar SolaceBase a ranar Juma’a, shugaban ayyuka na hukumar, Salisu Sale ya ce kukan daliban ya sa hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Sale ya ce kusan shekaru uku dalibai 120 na Kwalejin koyon aikin jinya da ke Danbatta har yanzu ba a tantance su ba saboda rashin biyansu kudaden da jami’in kula da aikin jinya Zubairu Idris ya yi.
‘’Danbatta Focal, Zubairu Idris ya yi zargin karkatar da kudaden dalibai 120 wanda ya jefa daliban cikin mawuyacin hali na kusan shekaru uku a lokacin Hajiya Hasiya Sani a matsayin shugabar makarantar,’’ inji Sale.
“Bayan mun kama shi tare da yi masa tambayoyi da bincike a hankali, ya amsa laifinsa kuma ya rattaba hannu kan yarjejeniyar mayar da kudin kafin mu gurfanar da shi a gaban kotu.
‘’ A halin yanzu ya biya kudin dalibai kusan 44 daga cikin 120’’.
SolaceBase ta ruwaito cewa Fadilu Aliyu Focal Person Madobi ya shaidawa masu binciken cewa an sanya kudin ne a cikin cryptocurrency kuma ya yi asarar kudaden acikin harkar.
