Connect with us

News

Masu Garkuwa Sun Bidige Mutum Daya Kai Musu Kudin Fansar Yan’uwan Sa Naira Miliyan 16 Da Babura 3

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rahotanni sun tabbatar da cewar matashin da aka tura ya Kai kudin fansar wasu mutane 9 da masu garkuwa suka sace,kudin da ya kai Naira miliyan 16 da babura 3 shima sun halaka shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa City and Crime ta fitar da rahotan cewar masu garkuwa sun fara da bukatar Nera miliyan 30 bayan da suka kwashe Mutanen 9, a Unguwar Iya a Jeren Jihar Kaduna, tun ranar 16, ga watan afurelun wannan shekarar ta 2024.

Dalilin Da Ya Sa Na Maida Makudan Dalolin Kasar Amurka Da Kuma Riyal Na Kasar Saudi Arebia Dana Tsinta A Makka – Alhajin Jigawa

Rahotan ya ce Wani makusanci ne ya tabbatar da manema Labarai cewar masu garkuwan sun daure tare da harbe Abbas, Dan kimanin shekaru 27, a lokaci guda bayan da suka karbe adadin kudaden daya Kai musu.

Rahotanni na nuni da cewa Daya daga cikin wadanda basu garkuwan suka saki, ya ce masu garkuwan sun bindige matashi Abbas, ne saboda wai lokacin da suke tattauna yarjejeniyar kudade da suke bukata a matsayin kudin fansa ya farfada musu maganganu Kuma yayi musu taurin Kai.

Zuwa yanzu jami’in Hulda da jama’a na rundunar Yan’sandan ta kasa reshen jihar Kaduna, ASP. Mansur Hassan bai ce komai ba game da batun.

Advertisement

To amma Shuaibu Hussain, makusanci ga Wanda aka kashe ya ce masu garkuwan sun Fadi inda aka je aka dauko gawar Abba da suka halaka.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending