Connect with us

News

Zargin Ɓatanci : An Hallaka Wani Mutumi A Jihar Bauchi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wasu fusatattun mutane a Bauchi sun hallaka wani mutum mai suna Yunusa a ranar Laraba bayan an zarge shi da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad.

Rahotanni na nuni da cewa Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana a unguwar Nasaru da ke ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Soke Dokar Da A Ka Yi Amfani Da Ita Wajen Rushe Sarakuna Biyar Na Jihar Kano.

Wani ganau mai suna Umar Abubakar shi ne ya shaida wa WikkiTimes ta wayar tarho cewa gardama ne ta ɓarke tsakanin Yunusa da wani mutum, inda Yunusa ya yi suɓul da baka ya furta kalaman batanci.

Sanadin haka ne ya jawo hankalin mutane suka rufu a kansu.

“Wanda aka kashe ya kasance dan kungiyar Islamic Faira ne. A lokacin da ya zagi Annabi, wasu samari suka kalubalanci shi Yunusa da ya janye maganarsa, amma ya ki, har ma ya sake maimaitawa. Daga nan ne suka fara masa da duka.” Inji Abubakar.

Advertisement

A cewar wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa saboda fargabar halin da ake ciki, ya ce ƴan sanda sun yi kokarin ceto wanda ake zargin zuwa ofishinsu kafin daga bisani matasan suka ci ƙarfin su har suka kashe shi

“Mutumin ya mutu ne a ofishin ‘yan sanda da ke Nasaru. Inda Daga baya suka kai gawar sa zuwa sashin ƴan sanda na Ningi, in ji shi, ya kara da cewa “’yan sanda ba su iya shawo kan ƴan ta’addan balle su iya hana su.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending