News
Mutum Biyu Sun Kamu Da Cutar Kwalara A Katsina, 118 Kuma Na Karɓar Kulawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina, ta ce an tabbatar da cutar kwalara ta kama mutum biyu a ƙaramar hukumar Kusada, da ke jihar tare da wasu 118 da a ke binciken lafiyarsu.
A cewar hukumar, tuni an ɗauki matakan fara amfani da tsarin kula da al’amuran da ke faruwa domin hana yaɗuwar cutar da sauran cutukan da za a iya rigakafinsu a jihar.
An gano Bullar Cutar kwalara a Jahar Katsina bayan ta yi ajalin mutum biyu
Daraktan kula da cutuka na hukumar, Dakta Kabir Sulaiman, a wani taron manema labarai a cibiyar bayar da agajin gaggawa ta hukumar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan shawo kan cutar.
Dakta Sulaiman ya ce jihar ta shirya tsaf don daidaita lamarin ɓullar cutar tare da samar da tsarin sa-ido don gano masu kamuwa da cutar.
Hukumar yaki da cutar kwalara ta duniya, ta bayyana Jihar Katsina a matsayin yankin da ke fama da cutar kwalara, inda ake ganin ƙananan hukumomi 10 suna cikin hatsarin kamuwa da ita.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
