News
Wata Babbar Motar Tirela Ta Kashe Masu Sallar Juma’a 14, Tare Da Raunata Da Dama A Kano.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane 14 tare da wasu da dama da suka samu raunuka bayan wata babbar motar dako (Tirela) ta kwace tare da kutsa kai cikin jama’ar dake Sallar Juma’a a Kano.
SolaceBase ta rawaito cewa hatsarin ya faru ne a dai-dai lokacin da ake Sallar Juma’a a wani Masallaci da ke garin Imawa a karkashin karamar hukumar Kura.
FRSC ta bayyana cewa Direban motar ya gaza sarrafa ta, lamarin da ya kai ga ta kwace, ta kutsa kai cikin mutanen da ke Sallah kusa da bakin hanya.
A jawabin da kwamandan FRSC a jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya fitar ta bakin kakakin hukumar, Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa sun samu labarin afkuwar lamarin da misalin karfe 1:30 na rana.
Jawabin ya kara da cewa ya zuwa yammacin ranar Juma’a an binne mutum tara daga cikin wadanda suka rasa ransu yayin da wadanda suka samu raunuka suna samun kulawa a asibiti.
FRSC ta bayyana cewa ta gaggauta aika jami’anta zuwa wurin da abin ya faru domin su bayar da agajin gaggawa da kuma kulawa ta musammam ga wandanda abin ya shafa.
Hukumar FRSC ta mika sakon ta’aziyyar ta ga iyalan wadanda suka rasa ransu.
