Connect with us

News

Hukumar NDLEA Ta Kama Matasa Maza Da  Mata 60 Da Suke Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, a ranar Lahadi, ta kai samame wani gida da matasa suke dabdalewar shaye-shayen kwayoyi da ganye inda ta kama mutane 60.

Advertisement

Kakakin hukumar Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kaiwa matasan samame bayan sun samu bayanan sirri game da wannan dabdalewa da suka shirya yi.

Abinda ya sa na ki karbar cin hancin naira miliyan 150 daga wani dan kasuwa –  Jami’an Dan Sanda

An kama mata 35 da wasu maza 25 maske sun rankwale da kwayoyi, suna bushe-bushe naɗaɗɗun mandula na wiwi da wasu kwayoyi.

Advertisement

Wasunsu an sake su bayan sun biya tara wasu kuma suna tsare hannun ƴan sanda.

Matasan dai suna bukin nuna wanda ya iya dakewa ne bayan ya yi matuƙar maskewa, ya haɗiyi kwayoyi batare da ya nuna gazawa ba.

Advertisement

An kama su a wani gida dake rukunin gidaje na Sun City dake Abuja.

A cikin matasan da aka kama an samu wasu mutum shida da ke ɗauke da wasu sunadarai na musamman na rankwalewa, waɗanda aka kama sun haɗa da Victoria Adoga, Hamza Yari, Joanne Essein, Socchima Valentine Jago Imole da Charles Indobuibisi.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Premium Times 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending