Connect with us

News

Yan bindiga sun sake kashe wani babban malamin jamia, tare dayin garkuwa da Ya’yansa

Published

on

DAGA MAHAMMAD MAHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan wani Babban malami a jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke jihar Katsina

Malamin, mai suna Dakta Tiri Gyan David, shi ne Shugaban sashen tattalin arziƙi na noma, bunƙasawa da raya Karkara a jami’ar FUDMA.

Lamarin ya faru ne a unguwar Lowcost Yarima Quarters da misalin karfe 1:30 na dare a ranar Talata,

Advertisement

Jaridar inda ranka ta rawaito ‘yan bindigar sun kashe malamin jamiar ne  tare da sace ‘ya’yansa guda biyu.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun dira a Unguwar ne da manyan makamai tare da yin harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Wani ganau ya shaida wa wakilmu  cewa harbe-harben da aka yi ya sa suka farka: “Mun shiga damuwa matuƙa, da misalin ƙarfe 1:35 na dare, sai muka ji ƙarar harbe-harbe ta ko’ina a Unguwar, daren ya kasance mana mai ban tsoro. Sai muka ji kuma an kashe wani malamin FUDMA, sannan an sace wasu daga cikinsu ‘ya’yansa”.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, Aliyu Sadeeq, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending