News
Rikicin masarautu :Kotu ta dage sauraron ƙarar da gwamnatin kano ta shigar kan tsohon sarki aminu ado –
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
wata babbar kotu a jihar Kano ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, inda za ta ci gaba da sauraren karar da gwamnatin Kano ta shigar tana bukatar tabbatar da Sarki Sunusi na biyu a kejerar sarauta.
Babban lauyan gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar ta bakin Lauyan su Ibrahim Isah-Wangida suka shigar da karar a ranar 27 ga watan Mayu.
DCL Hausa ta rawaito cewa gwamnatin tana neman a bada umarnin hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tube daga sarautar Bichi, Rano, Gaya da Karaye bayyana kansu a matsayin sarakunan gargajiya.
Sauran wadanda aka yi ƙarar su sun hada da Sufeto-Janar na ’Yan sanda, Daraktan jami’an tsaro na farin kaya a Jiha, da jami’an tsaro na Civil Defence da Sojojin Nijeriya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
