News
Yan bindiga sun sake kashe wani babban malamin jamia, tare dayin garkuwa da Ya’yansa
DAGA MAHAMMAD MAHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan wani Babban malami a jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke jihar Katsina
Malamin, mai suna Dakta Tiri Gyan David, shi ne Shugaban sashen tattalin arziƙi na noma, bunƙasawa da raya Karkara a jami’ar FUDMA.
Lamarin ya faru ne a unguwar Lowcost Yarima Quarters da misalin karfe 1:30 na dare a ranar Talata,
Jaridar inda ranka ta rawaito ‘yan bindigar sun kashe malamin jamiar ne tare da sace ‘ya’yansa guda biyu.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun dira a Unguwar ne da manyan makamai tare da yin harbe-harben kan mai uwa da wabi.
Wani ganau ya shaida wa wakilmu cewa harbe-harben da aka yi ya sa suka farka: “Mun shiga damuwa matuƙa, da misalin ƙarfe 1:35 na dare, sai muka ji ƙarar harbe-harbe ta ko’ina a Unguwar, daren ya kasance mana mai ban tsoro. Sai muka ji kuma an kashe wani malamin FUDMA, sannan an sace wasu daga cikinsu ‘ya’yansa”.
Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, Aliyu Sadeeq, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
