News
‘Yan Sanda Sun Ceto Yaro Dan Shekara 5 Da Aka Daure Da Sarka Tare Shafe Kwanaki Uku Ba Abinci
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun ceto wani yaro dan shekara 5 da mahaifinsa ya daure shi da sarka kuma ya bar shi cikin yunwa na tsawon kwanaki uku.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa An ceto yaron ne bayan samun wani rahoto daga makwabtan da abin ya shafa a unguwar Gwallagan Mayaka a cikin babban birnin Bauchi.
Jami’an ‘yan sandan sun samu labarin cin zarafin yaron ne a ranar 3 ga watan Yuli, 2024, lokacin da Dagacin kauyen Gwallagan Mayaka da ke Bauchi ya ba da rahoton cewa ya samu labari daga wani saurayi .
wanda ya bayyana cewa matarsa ta sanar da shi cewa ta ga wani yaron makwabcinsu dan shekara 5 an daure shi da sarka a cikin wani daki.
Da sauri Amina ta duba yaron don tabbatar da halin da yake ciki, ta same shi kwance a sume, an daure shi da sarka.
Kakakin Rundunar SP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Bauchi ranar Juma’a, inda ya ce bayan samun labarin, tawagar jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Mubarak S. Baba, DPO na Dutsen Tanshi ta koma ofishin ‘yan sanda wurin da ya ceto yaron.
Sanarwar ta bayyana cewa yayin wata tattaunawa da aka yi da shi, wanda abin ya shafa Hussaini Abubakar, ya bayyana cewa mahaifinsa mai suna Abubakar Nuhu, mai shekaru 50, wanda aka fi sani da Wanzam na Gwallagan Mayaka ya ci zarafinsa.
Yaron ya kuma bayyana cewa mahaifinsa ya tsare shi, inda ya yi kwana uku babu abinci.
A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya umurci jami’in dan sandan shiyyar DPO da ya kama wanda ya aikata laifin domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa aikata laifin.
Wakil ya ce yayin da ake yi masa tambayoyi, an kama wanda ake zargin, Abubakar Nuhu wanda aka fi sani da Wanzam da laifin cin zarafin yara.
Wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa ya tsare yaron ne domin ya hukunta shi saboda satar kayan makwabcinsu kuma wani abokinsa ya ba shi shawarar yin hakan.
Kakakin’yan sandan ya ce CP ya umurci DPO da ya mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, CID, kuma ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashen da ya binciki lamarin cikin hikima da kuma wasu dalilai da suka sa aka aikata wannan ta’asa.
