Connect with us

News

Shin ko mahaifiyar dauda kahutu rara tana raye bata mutuba Aisha humaira ta magantu Kan wannan lamarin 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Tun bayan sace mahaifiyar dauda kahutu rara da Yan bindinga sukayi tsahon kwanaki takwas al,umma da dama a shafukan sada zimunta keyiwa fitaccen mawakin jaje inda wasu Kuma keyin San barka da hakan

Advertisement

Ana ganin dai Jama,a da dama natayin faranciki ne sakamakon Yadda mawakin ke yaban gwamnatin duk kuwa da barazanar tsaro da talaucin data addabi  Al,uummar

Saidai Kuma Jaruma a masana’antar Kannywood, kuma ta kusa da mawaki Dauda Kahutu Rarara, Aisha Humaira ta mayar da martani kan wadanda suke yi wa mahaifiyar mawakin da yan bindaga suka sace a gidanta da ke garin Kahutu na karamar Hukumar danja dake Jihar Katsina muguwar fata, dangane wannan jarabawa da ta same mawakin

Advertisement

 

Humaira a wani faifan bidiyo data wallafa a shafinta na Tik Tok ta fara da godiya da fatan alheri ga wadanda suka nuna damuwarsu kuma suka jajanta wa Rarara kan wannan iftila’in da ya samu mahaifiyarsa.

Advertisement

Daga nan sai ta ce tana matukar mamaki da kaico kan wasu mutane da suke yi wa mahaifiyar mawakin muguwar fata don kawai Rarara ya yi wani abin da ya bata masu rayuwa. Ko Kuma sabanin ra,ayoyin su

 

Advertisement

Na tabbatar da cewar duk wanda ya san halayyar mahaifiyar mawakin ba zai yi mata wani fata mai muni ba, saboda bai war Allah ce da ta rike addinin Musulunci hannu bibiyu kuma take salatin ga Annabi a mafi yawan lokuta.

Aisha ta kara da cewar mahaifiyar mawakin a ko da yaushe tana yi masa nasiha kan ya ciyar da mutane daga cikin abin da Allah ya hore masa na dukiyarsa domin kuwa duk abin da ka bai wa wani a nan duniya Allah zai biyashi a ranar gobe kiyama.

Advertisement

A cewarta, takan dinga yi masa nasiha tana cewa ina za ka kai kudin da Allah ya hore maka idan har ba ka taimaki al’ummar Annabi ba, kasani Allah ya ba ka wannan dukiya ne domin wasu su samu ta hanyarka ba don ka dinga ci kai kadai ba.

Dangane da zamanta a kauyen Kahutu kuwa, Aisha ta tabbatar da cewa babu yanda Rarara bai yi da mahaifiyar tasa ba kan ta koma Kano da zama, amma ta ki yarda, inda ta nuna ta fi jin dadin zama a cikin ‘yan’uwa da abokan arziki da aka taso tare tun ana yara.

Advertisement

Humaira ta bukaci mutane da su dinga yi wa iyayen wasu fatan alheri domin kuwa duk abin da ka yi wa iyayen wasu shi za a yi wa naka iyayen, kuma babu wanda ya isa ya gujewa kaddara, duk abin da Allah ya nufa kan mutum dole sai ya faru komai dabarar wannan mutumin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending