Connect with us

News

Shugabannin Ƙasashen Burkina Faso, Mali Da Nijar Na Taron Ƙungiyar A Karon Farko 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A karon farko, ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali suna gudanar da taron ƙungiyar Sahel Alliance AES a Niamey babban birnin Nijar.

Advertisement

Tun a ranar Juma’a da yammaci Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore ya isa Niamey inda ya samu kyakkyawar tarba daga Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani da muƙarrabansa.

Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Yayin Da Mata Da Yara Suke Kuka, Sun Yi Barazanar Kai Sabon Hari

Haka kuma Tiani zai karɓi baƙuncin Assimi Goita a ranar Asabar ɗin kafin soma taron.

Advertisement

Fadar shugaban kasar Burkina Faso ta ce “yaki da ta’addanci” da “karfafa hadin gwiwa” za su kasance cikin ajandar ranar Asabar, duba da irin munanan hare-haren ta’addanci da kasashen uku ke fuskanta.

Duka shugabannin ƙasashen uku sun bar ƙungiyar ECOWAS a watan Janairu inda suke zargin ‘yar amshin shata ce ta Faransa haka kuma ba ta yin abin da ya dace wurin daƙile masu iƙirarin jihadi.

Advertisement

Su ma shugabannin na ECOWAS za su yi taro a Nijeriya a ranar Lahadi domin tattaunawa kan dangantakarsu da ƙungiyar ta Sahel Alliance.

A watan Maris ne ƙungiyar ta AES ta sanar da shirinta na yaƙi da masu iƙirarin jihadi, duk da cewa ba ta fito ta bayyana hanyoyin da za ta bi ba.

Advertisement

Haka kuma duka shugabannin ƙasashen uku sun ja layi tsakaninsu da tsohuwar uwar goyonsu wato Faransa inda suka kori sojojinta da ke zaune a ƙasashen inda suka ƙulla ƙawance da Rasha.

Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun shafe shekaru sun fuskantar hare-haren ta’addanci musamman a yankin da ƙasashen uku suke da iyaka, inda ƙungiyoyin da ke da alaƙa da IS ke kashe farar hula da kai hari ga sojoji inda suke raba miliyoyin jama’a da muhallansu.

Advertisement

 

AFP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending